logo

HAUSA

Kasar Sin ta gayyaci jakadan EU don nuna bacin ranta game da takunkumin da kungiyar ta kakaba mata kan batun Xinjiang

2021-03-23 16:25:24 CRI

A yau ne, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya gaggaci jakadan kungiyar Tarayyar Turai (EU) dake kasar Sin Nicolas Chapuis, don gabatar da koken kasarsa, kan takunkumin da kungiyar ta kakaba mata kan batun Xinjiang.

Mataimakin ministan, a madadin gwamnatin kasar Sin, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan takunkumi na gaira babu dalili da EU din ta kakabawa kasarsa, ta hanyar fakewa da batutuwan da suka shafi hakkin dan-Adam a yankin Xinjiang.

Qin ya shaidawa jakadan cewa, kasar Sin za ta mayar da martanin da ya dace, yana mai nuni da cewa, takunkumin da kungiyar ta kakabawa kasar Sin, ta yi shi ne kawai bisa dogaro kan karya da bayanai marasa tushe kan Xinjiang, wadanda suka ci karo da shaidu, da dokoki da bayanai na zahiru game da yankin. (Ibrahim Yaya)