logo

HAUSA

Sin ta kakabawa wasu mutane da kamfanonin Turai takunkumi

2021-03-23 10:17:40 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce kasar ta kakabawa wasu mutane 10, da kamfanonin Turai 4 takunkumi, sakamakon yadda suka yi matukar lahanta moriyar kasar ta Sin, kana suka yada karairayi, da farfaganda maras tushe game da kasar.

Ma’aikatar wajen ta ce, a jiya Talata, kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta kakabawa wasu Sinawa da kamfanonin kasar takunkumi, bisa zargin Sin da keta hakkokin bil Adama a jihar Xinjiang.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin ma’aikatar wajen Sin ya ce matakin EU ya biyo bayan karairayi, da jita jita, da jirkita gaskiya, tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin. Baya ga watsi da kungiyar ke yi da dokokin kasa da kasa da ka’idojin cudanyar kasa da kasa, kungiyar ta gurgunta alakar da ke tsakanin Turai da Sin.

Kakakin ya kara da cewa, wajibi ne EU ta yi watsi da halayyar munafurci, da fuska biyu, tare da dakatar da bin hanya maras bullewa, idan kuwa ba haka ba, Sin za ta ci gaba da maida martani da ya wajaba.  (Saminu)

Saminu