logo

HAUSA

Jami’ar Ji’nan za ta fitar da rahoto game da ma’aikata kananan kabilun Xinjiang dake sauran wuraren kasar Sin

2021-03-19 16:44:22 CRI

Jami’ar Ji’nan za ta fitar da rahoto game da ma’aikata kananan kabilun Xinjiang dake babban yankin kasar Sin_fororder_210319-jami'ar Jinan

A dangane da rahoton da Bajamushen nan makiyin kasar Sin mai suna Adrian Zenz ya wallafa, wanda wasu kamfanoni da jama’a a yankin Xinjiang na kasar Sin suke shirin kai shi kara, masanin ya sake wallafa “wani sabon rahoto” mai taken “yadda ake tilasta ’yan kwadago yin aikin dole da tilasta musu barin yankunansu da sunan sauya wurin aiki a Xinjiang”. Ya ce “an yi haka ne don rage yawan al’ummar ’yan kabilar Uygur” da “kawo matasa cikin yankin ’yan kabilar Han”.

Shin ina gaskiyar binciken da Adrian Zenz da sauran makiya kasar Sin suka yi kan wannan batu? Shin wane hali ’yan kwadago na kananan kabilu suke ciki a babban yankin kasar Sin? A kwanakin nan ne, cibiyar nazarin harkokin sadarwa da shugabanci game da kan iyaka ta jami’ar Ji’nan ta shirya fitar da wani rahoton bincike mai taken “Batun tilasta aikin kwadago ko kokarin neman rayuwa mai kyau--halin da ’yan kwadagon Xinjiang suke ciki a babban yankin kasar Sin” domin yin bayani dalla-dalla, game da halin da ma’aikata kananan kabilun yankin Xinjiang dake aiki a Guangdong suke ciki.

Sai dai ba kamar yadda Adrian Zenz da sauran makiya kasar Sin suka kitsa irin wannan rahoto na karya, ba tare da gudanar da cikakken bincike ba, wannan rahoton da jami’ar Ji’nan take shirin fitarwa, ya gudanar da cikakken bincike, kan wasu kamfanoni biyar da ma’aikatan kananan kabilun yankin Xinjiang suke aiki a Guandong (ciki har da wasu kamfanoni biyu da shi Adrian Zenz ya ambata a rahotonsa) aka kuma zanta da ma’aikatan kananan kabilun Xinjiang, ciki har da na Uygur da Khazak, da Tajik. Baki daya an zanta da ma’aikatan kananan kabilu 70, inda aka fahimci dalilin da ya sa irin wadannan rukunin ma’aikata suke aiki a kamfanonin dake babban yankin kasar Sin, da yadda suke rayuwarsu ta yau da kullum, da muhimmancin da kwarewar da za su samu za ta yi ga yankin Xinjiang a nan gaba da kuma shirinsu a rayuwa.

A karshe rahoton jami’ar ta Ji’nan, ya kuma yi nuni da cewa, wannan zabinsu ne na kashin kai, na yin aiki a wajen yankin nasu. Haka kuma, kamfanonin da suke aikin, ya kiyaye duk wani ’yancin ’yan kwadago na kananan kabilu yankin Xinjiang . Bugu da kari, kananan kabilu ma’aikata daga yankin na Xinjiang, suna da ’yancin bin addini, da ’yancin magana da yarensu, da zabin wurin da za su zauna, baya ga ’yancin da suke da shi na kiyaye tsarinsu na addini da na abinci, an kuma yi wani tsari na samar musu abincin halal a wadannan kamfanoni. (Ibrahim Yaya)