logo

HAUSA

Wasu kamfanoni da al’ummomin jihar Xinjiang za su gabatar da kara kan dan kasar Jamus Adrian Zenz da BBC

2021-03-18 13:58:48 CRI

Yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai game da batutuwan jihar Xinjiang, inda aka bayyana cewa, wasu jami’ai da al’ummomin jihar Xinjiang ta kasar Sin sun yi Allah wadai da rahoton da dan kasar Jamus Adrian Zenz ya fidda game da jihar Xinjiang. Ban da haka kuma, a halin yanzu, wasu kamfanoni da al’ummomin jihar sun shigar da karar Adrian Zenz da kamfanin dillancin labarai na BBC ta hannun lauyarsu.

Mataimakin shugaban Sashen fadakar da jama’a na jihar Xinjiang Xu Guixiang ya ce, an samu babbar nasara a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da bata taba ganinsu a tarihi ba a jihar Xinjiang, al’ummomin jihar sun gamsu matuka. Kuma, dukkanin kasashen duniya sun ganewa idanunsu game da babbar bunkasuwar da wannan jiha ta samu, ba wanda zai saurari karyar da Adrian Zenz ya fadi. (Maryam)