logo

HAUSA

Mata ‘yan kabilar Uygur sun karyata rahotannin karya da kafofin watsa labaran kasashen yamma suka bayar kan Xinjiang

2021-03-17 19:11:16 CRI

A ranar 15 ga wata, wakilai mata ‘yan kabilar Urgur, Yilixinna da Tusongnisha Aili, sun gabatar da jawabi daya bayan daya, a zama na 46 na hukumar kiyaye hakkin dan Adam ta MDD, inda suka bayyana yadda mata ‘yan kabilar Uygur suke jin dadin rayuwa a jihar Xinjiang ta kasar Sin, kuma sun karyata rahotannin karya da wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka bayar kan jihar.

Yilixinna ta ce, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma, sun zargi jihar Xinjiang da cewa, wai babu hakkin dan Adam a jihar. To sai dai kuma, tun bayan aka haife ta a jihar, abubuwan da ta gani da idonta, sun sha bamban da abubuwan da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suke wallafa. Alal misali, a yayin bukukuwan gargajiya na jihar Xinjiang, kamar su babbar sallah da karamar sallah, dukkan su suna yin hutu, kuma ko wace rana, kakarta mai shekaru 90 da haihuwa, tana kallon shirye-shiryen yaren Uygur ta telibijin.

Yilixinna ta kara da cewa, jihar Xinjiang wuri ne mai dacewa da jin dadin rayuwa, tana kuma fatan za a daina lahanta moriyar wurin, kuma a daina lahanta zumuncin dake tsakanin kalibu daban daban na kasar Sin.

A nata bangare, Tusongnisha Aili ta bayyana cewa, ita kanta, daliba ce da ta kammala karatu a cibiyar horas da sana’o’i ta gundumar Hetian ta jihar, kuma daliban dake karatu a cikin cibiyar suna koyon yaren Han, da ilmomin dokoki, da kuma kwarewar sana’o’i baki daya.

Ta ci gaba da cewa, bayan kammala karatu a cibiyar horaswar, ta yi aiki a wani kamfanin dinkin tufafi, har ta zama darekatar sashen dinkin tufafi a kamfanin. Sakamakon kwarewarta, kudin shigarta a ko wane wata ya kai kudin Sin yuan 4000, don haka sharadin rayuwarta ya kyautata, tana kuma jin dadin rayuwa tare da iyalanta.  (Jamila)