logo

HAUSA

Carrie Lam Cheng Yuet-ngor: Hong Kong Za Ta Ci Gaba Da Samun Kwanciyar Hankali Da Wadata Sakamakon Kyautatuwar Tsarin Harkokin Zabe A Yankin

2021-03-09 14:05:48 CRI

Carrie Lam Cheng Yuet-ngor: Hong Kong Za Ta Ci Gaba Da Samun Kwanciyar Hankali Da Wadata Sakamakon Kyautatuwar Tsarin Harkokin Zabe A Yankin_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_6012_e14c7188-2457-49e6-a328-eef569ec3a31

Yayin da kantomar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor take zantawa da wakilinmu a kwanan baya, ta ce, ta yi farin ciki da ganin gwamnatin tsakiya ta kyautata tsarin harkokin zabe a yankin da kuma aiwatar da ka’idar “tabbatar da ganin ’yan kishin kasa sun gudanar da harkokin yankin Hong Kong”. Tana mai cewa, Hong Kong za ta ci gaba da samun kwanciyar hankali da wadata. Ta ce a nan gaba, Hong Kong za ta shiga ayyukan raya kasa cikin himma yayin da gwamnatin take aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14.

Yayin da take zantawa da wakilinmu, kantomar Hong Kong ta ce, yadda gwamnatin tsakiya ta kyautata tsarin harkokin zabe da aiwatar da ka’idar “Tabbatar da ganin ’yan kishin kasa sun gudanar da harkokin yankin Hong Kong” ya samar da cikakken goyon baya. Aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin na Hong Kong a bara ya kwantar da kura a yankin. Baya ga samun kwanciyar hankali a zamantakewar yankin, dole ne a samu kwanciyar hankali a harkokin siyasa. Kyautata tsarin harkokin zabe a Hong Kong ya ba da tabbaci wajen wanzar da kwanciyar hankali a harkokin siyasa. Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor ta ce, “A gani na, mun samu cikakken goyon baya. Aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong a bara ya kwantar da kura a yankin. Baya ga samun kwanciyar hankali a zamantakewar yankin, dole ne a samu kwanciyar hankali a harkokin siyasa. Ta yaya za a tabbatar da tsarin siyasa yadda ya kamata a yankin na Hong Kong? Ta yaya za a hana marasa kishin kasa shiga tsarinmu na siyasa? Ta yaya za a hana su hada hannu da wasu kasashe don illata tsarin siyasar Hong Kong, a yunkurin ta da kura a yankin? Yadda gwamnatin tsakiya ta kyautata tsarin harkokin zabe ya ba da tabbaci ga harkokin siyasar yankin.”

Dangane da kulawar da kasashen duniya suke nunawa kan kyautata tsarin harkokin zabe a Hong Kong, kantomar ta ce, a matsayinta na wani babban birni, Hong Kong za ta ci gaba da samun kwanciyar hankali da wadata sakamakon goyon bayan gwamnatin tsakiya, da samun kwanciyar hankali a zamantakewa da tsarin siyasa. Inda ta ce, “Wasu kamfanoni baki da kasashe, sun yi imani da makomar Hong Kong. A ganinsu, Hong Kong na da kyakkyawar dama muddin ta shiga manyan ayyukan gwamnatinmu na raya kasa. Mun yi na’am da ra’ayoyinsu. Bayan da aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong, za a tabbatar da ganin ’yan kishin kasa sun gudanar da harkokin yankin, yanzu Hong Kong ta samu kwanciyar hankali a zamantakewa da tsarin siyasa. Kuma za ta ci gaba da samun kwanciyar hankali da wadata bisa goyon bayan gwamnatin tsakiya kuma a karkashin manufar ‘kasa daya mai tsarin mulki biyu’. Yankinmu na Hong Kong na bude kofa ga kowa, muna maraba da zuwan kowa don shiga ayyukan raya yankin.”

Dangane da makomar yankin, kantomar ta ce, shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14 yana da ma’ana mai zurfi ga Hong Kong. Hong Kong za ta yi amfani da zarafin don shiga ayyukan raya kasa. Inda ta ce, “An tanadi Hong Kong cikin wannan shiri. Hakika dai Hong Kong ta riga ta shiga ayyukan raya kasa sosai. Na yi farin ciki da ganin gwamnatin tsakiya za ta goyi bayan raya yankin Hong Kong zuwa wata cibiyar kasa da kasa a fannoni 3, wato cibiyar kasa da kasa ta zirga-zirgar jiragen sama, cibiyar kasa da kasa ta kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, da cibiyar mu’amalar al’adu da fasaha. Akwai kalmomi dari 5 a cikin wannan shiri, amma sun shafi fannoni daban daban. Don haka nan da shekaru 5 masu zuwa za mu yi amfani da wannan zarafi yadda ya kamata.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan