logo

HAUSA

Kwararren Morocco: Kyautata tsarin zabe na Hong Kong zai samarwa yankin tabbacin zaman lafiya da ci gaba

2021-03-08 20:25:01 CRI

Kwararren Morocco: Kyautata tsarin zabe na Hong Kong zai samarwa yankin tabbacin zaman lafiya da ci gaba_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_1_fe643d16-0438-4c4d-b53a-386fb304deb5

A yayin zama na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13 wanda a yanzu haka yake gudana a Beijing, za’a yanke shawara kan kyautata tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong, abun da ya kasance wani muhimmin mataki na daban da aka dauka don inganta dokokin shari’a gami da tsarin siyasa na Hong Kong bisa kundin tsarin mulkin kasar.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar hadin-kai da neman ci gaba tsakanin Afirka da kasar Sin ta kasar Morocco Nasser Bouchiba ya bayyana cewa, kyautata tsarin zaben Hong Kong zai samarwa yankin tabbacin zaman lafiya da bunkasuwa mai dorewa.

Nasser Bouchiba ya ce, bayan shafe sama da shekaru 20 ana kokari, an samu manyan sauye-sauye a yanayin da ake ciki da wajen yankin Hong Kong, abun da ya bukaci a kara kyautata dokoki gami da ka’idoji bisa sabon halin da ake ciki. A wani bangaren, matakin zai tabbatar da cewa, masu kishin Hong Kong za su iya mulkar wajen, da hana shisshigin da wasu daga kasashen waje suka yi, don rage kawo illa ga Hong Kong. A daya bangaren kuma, hakan zai taimakawa al’ummar Hong Kong samun damar neman ci gaba cikin sauri kuma daga dukkan fannoni tare da babban yankin kasar.(Murtala Zhang)