logo

HAUSA

Ya zama dole a kyautata tsarin zabe a yankin Hong Kong

2021-03-05 15:41:23 CRI

An gabatar da ajandar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na bana a daren ranar 4 ga wata, wadda ta nuna cewa, wani muhimmin batun da za a tattauna a yayin taron shi ne daftarin kudurin kyautata tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong.

Akwai matsala a cikin tsarin zaben yankin Hong Kong na yanzu, domin ba a iya tabbatar da ‘yan takara na yankin da suka dace da ma’aunin kaunar kasa. Wasu masu tada zaune tsaye da kin jinin kasar Sin ko ‘yan aware na yankin, suna amfani da zaben don shiga hukumomin mulkin yankin, inda suke yada ra’ayoyin aware, da kawo cikas ga tattauna harkokin yankin da kuma yi wa hukumar kafa doka tarnaki, hakan ya sa an ajiye batutuwa da dama dake shafar tattalin arziki da zaman takewar jama’ar kasar a yankin da gaza daidaita su, da kawo babbar illa ga zamantakewar al’ummar yankin, har ma da mayar da yankin Hong Kong matsayin wuri mai hadari na kasar Sin a fannin tsaron kasa.

Babu kasar da zata amince da ayyukan ‘yan aware. A matsayin hukumar koli ta kasar Sin, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta tsaida kudurin kyautata tsarin zaben yankin Hong Kong bisa tsarin mulkin kasar, wannan ikonta ne kuma nauyi ne dake wuyenta.

Don girmama ra’ayoyin jama’a, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gudanar da shawarwarin jin ra’ayoyin jama’a sau da dama don sauraron ra’ayoyin wakilan yankin Hong Kong daga bangarorin masana’antu, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da kwararru, da kwadago da sauransu.

Bayan yankin Hong Kong ya koma karkashin mulkin kasar Sin, an aiwatar da manufofin kasa daya mai tsarin mulki biyu, da ba mutanen yankin Hong Kong damar aiwatar da harkokinsu da kansu, da cin gashin kan yankin. Mazaunan yankin sun samu hakki da ‘yancinsu na demokuradiyyar. Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta tsaida kudurin kyautata tsarin zaben yankin a wannan karo don tabbatar da tsarin demokuradiyya ya bunkasa yadda ya kamata. (Zainab)