logo

HAUSA

Wang Yi: “A bari ‘yan kishin kasa su gudanar da harkokin yankin Hong Kong” halastacce ne kuma ya dace

2021-03-07 18:26:59 CRI

Inganta tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong da kuma aiwatar da ka’idar“A bari ‘Yan kishin kasa su gudanar da harkokin yankin Hong Kong” ya dace da kundin tsarin mulki kuma yana bisa doron doka kana yana da babbar ma’ana, mamban majalisar gudanawar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, shi ne ya bayyan hakan a yau Lahadi.

Wang ya ce, nuna kauna ga yankin Hong Kong daidai yake da nuna kauna ga kasar Sin, kasancewar yankin musamman na Hong Kong wani bangare ne kasar Sin.

Ya kara da cewa, kasar Sin zata cigaba da amincewa da manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu, inda a karkashin wannan manufar, al’ummar yankin za su gudanar da al’amurransu bisa cikakken ‘yancin na cin gashin kai.(Ahmad)