logo

HAUSA

Isra’ila ta fara kera na’urar kakkabo makamai masu linzami tare da Amurka

2021-02-19 11:06:06 CRI

A jiya ne kasar Isra’ila ta sanar da cewa, ta fara kera na’urar kakkabo makamai masu linzami dake cin dogon zango, mai suna Arrow-4 tare da kasar Amurka.

Da take karin haske kan haka, ma’aikatar tsaron kasar, ta ce, Arrow-4, za ta kasance wata na’ura ta zamani da aka kirkiro, wadda da za ta iya kakkabo makamai masu linzami, tana kuma da karfin magance dimbin barazana da yankin yake fuskanta, za kuma ta maye gurbin Arrow-2 cikin gomman shekaru dake take.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya