logo

HAUSA

Firaministan Isra'ila ya amince da yarjejeniya don kaucewa sabon zabe

2020-08-24 11:48:51 cri

Jiya Lahadi firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa ya amince da dage wa'adin kasafin kudin kasar, lamarin da zai kawo jinkirin babban zaben kasar wanda ake sa ran gudanarwa a kasa da shekaru biyu.

A jawabin da ya gabatarwa jama'ar kasar, ya ce, "Yanzu lokacin hadin kai ne, ba lokacin zabe ba".

Netanyahu ya ce, yana goyon bayan kudurin dage wa'adin amincewa da kasafin kudin kasar da karin kwanaki 100. Ya ce wannan yarjejeniyar da aka amince ita ce mafita ga tattalin arzikin Isra'ila a wannan lokaci.

Karkashin dokar Isra'ila, idan gwamnati ba ta amince da kasafin kudin kasa cikin kwanaki 90 bayan kafa ta ba, to majalisar dokokin kasar ta rushe nan take. A wannan karon wa'adin zai kare ne a daren ranar Litinin.

Netanyahu da babban abokin shugabancinsa, Benny Gantz, kana shugaban jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayin rikau, ya kamata su amince da kasafin kudin kasar a tsakar daren Litinin.

Sabon kudirin dokar zai ba su karin kwanaki 100 wajen cimma matsaya game da kasafin kudin kasar.

Netanyahu na fuskantar shari'a kan zarge-zargen aikata rashawa, da yin almundahana gami da cin amanar kasa, cikin zarge-zargen uku da ake tuhumar. Sai dai ya sha musunta tuhume-tuhumen da ake masa game da aikata ba daidai ba.

A watan Yuni aka fara shari'ar da ake yi masa, amma ya gaza yin murabus daga mukaminsa, duk da irin zanga-zangar da dubban 'yan kasar ke gudanarwa a duk fadin Isra'ilan inda suka bukaci shugaban ya sauka daga mukaminsa. (Ahmad)