logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya karbi gudummawar alluran rigakafin COVID-19 dubu 200 daga kasar Sin

2021-02-16 16:05:42 CRI

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, jiya Litinin ya karbi gudummawar alluran rigakafin COVID-19 dubu 200 a hukumance, da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasarsa.

Da yake jawabi yayin bikin karbar gudummawar rigakafin da jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun ya mika a fadar gwamnati dake Harare, shugaba Mnangagwa, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna kudirinta na taimakawa kasarsa a yakin da take yi da annobar COVID-19. Ya kuma bayyana godiya ga kasar Sin, kan yadda a ko wane lokaci take kasancewa tare da al’ummar Zimbabwe.

Mnangagwa ya ce, taimakon ya kara nuna jagoranci na gari da kasar Sin take ci gaba da yi, a kokarin da duniya ke yi na hana yaduwar kwayar cutar.

A nasa jawabin, jakada Guo, ya bayyana cewa, gudummawar alama ce ta zumuncin mai karfi dake tsakanin Sin da Zimbabwe. Yana mai cewa, kasar Sin ce kasa ta farko, da ta cika alkawarinta na mayar da alluran rigakafin a matsayin kayan al’ummar duniya.

Yanzu haka dai, kasar ta Zimbabwe ta sayi alluran rigakafi 600,000 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin, ana kuma sa ran za su iso kasar a watan Maris.(Ibrahim)