logo

HAUSA

Tallafin rigakafin COVID-19 da Sin ta baiwa Zimbabwe zai agaza wajen cimma nasarar yaki da annobar

2021-02-12 16:49:50 CRI

Ministar ma’aikatar watsa labarai a Zimbabwe Monica Mutsvangwa, a madadin kasar ta, ta yabawa gudummawar rigakafin COVID-19 da Sin ta baiwa Zimbabwen, tana mai cewa hakan ya taimakawa kasar, a yakin da take yi da wannan annoba.

Uwargida Mutsvangwa, wadda ta yi tsokacin yayin wani taron manema labarai da kafar watsa labaran kasar Sin, ta ce gwamnatin Zimbabwe, na matukar godiya ga kasar Sin, bisa kyautar alluran rigakafin Sin har 200,000, alluran da nan gaba kadan, za a yiwa jami’an lafiya mafiya fuskantar hadarin kamuwa da cutar ta COVID-19.

Jami’ar ta ce, tsarin gwamnati mai inganci, shi ke samar da daidaito a fannin siyasa. Kuma karkashin shugaba Mnangagwa, ana ci gaba da aiwatar da sauye sauye a fannin hada hadar kudade, da harkar zuba jari.

A daya bangaren kuma, an tsara kasancewar Zimbabwe a wani mataki mai tasiri, cikin yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA da aka kaddamar. Don haka a cewar ministar, hakan dama ce ga Sinawa masu sha’awar zuba jari, da su kara yawan jarin su a kasar dake kudancin Afirka.  (Saminu)