logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya yaba da gudunmuwar alluran rigakafin COVID-19 da Sin ta ba kasar

2021-02-13 16:21:18 CRI

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya godewa kasar Sin bisa gudunmuwar alluran rigakafin COVID-19 da ta ba kasarsa.

Da yake zantawa da kafar yada labarai ta kasar Sin, shugaba Mnangagwa ya ce, gudunmuwar alama ce ta daddadiyar dangantakar dake tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Zimbabwe za ta karbi gudunmuwar alluran rigakafi 200,000 daga kasar Sin a ranar Litinin, wanda zai zama na farko da kasar ta karba yayin da take kara himmantuwa wajen dakile yaduwar cutar.

Emmerson Mnangagwa, ya ce gudunmuwar za ta ishi dukkan jami’an lafiya dake aikin dakile cutar, inda za a yi amfani da ragowar wajen yi wa rukunoni masu rauni, kamar tsoffi da wadanda ke fama da wasu cututtuka.

Shugaban na Zimbabwe ya kuma bayyana yakinin rigakafin zai taimakawa Zimbabwe shawo kan cutar, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron lafiyar al’ummarta.

Tuni Zimbabwe ta kammala shirin karbar rigakafin da za a yi wa mutane a kallla miliyan 10, wato kusan kaso 60 na al’ummarta. (Fa’iza Mustapha)