logo

HAUSA

Gudunmawar rigakafin COVID-19 na Sin ya isa Zimbabwe

2021-02-15 17:21:17 CRI

 

Gudunmawar rigakafin COVID-19 na Sin ya isa Zimbabwe_fororder_11

Jirgin saman dake dauke da alluran rigakafin annobar COVID-19 wanda kasar Sin ta bayar gudunmawa ga kasar Zimbabwe ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Robert Mugabe dake Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, da misalin karfe 5:40 na safiyar yau Litinin, agogon kasar.

 

Gudunmawar rigakafin COVID-19 na Sin ya isa Zimbabwe_fororder_33

Da yake jawabi a filin jirgin, mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga, ya ce, kasar Sin ta jima tana taimakawa Zimbabwe domin yaki da annobar COVID-19, kuma gudunmawar rigakafin zai taimakawa kasar Zimbabwe a yakin da take da annobar kuma zai baiwa kasar damar farfado da harkokin tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a kasar.

Da yake jawabi a madadin kasar Sin, jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, ya ce, Sin ita ce kasa ta farko a duniya da ta mayar da hankali wajen samar da rigakafin COVID-19 don taimakawa al ‘ummar duniya. Zimbabwe tana daga cikin kasashen duniya da suka samu gudunmawar alluran rigakafin COVID-19 daga kasar Sin bisa mataki na farko, wanda hakan yana kara nuna yadda kyakkyawar alaka da aminantaka take a tsakanin kasashen biyu.(Ahmad)