logo

HAUSA

A Kiyaye Rayukan Mutane A Maimakon Yi Sukar Kasar Sin

2021-02-07 08:13:01 CRI

Kwanakin baya, jaridar The New York Times ta wallafi wani bayani mai taken “Shin kokarin kasar Sin na yaki da annobar COVID-19 ya zarce yadda ake bukata?”, inda aka yi sossoki kokarin da kasar Sin take yi wajen yaki da annobar, har ma a karshen bayanin, an rubuta cewa, nasarar da kasar Sin ta samu wajen yaki da annobar ta sanya ta shiga uku, wato jama’arta ba su yi taka tsan-tsan kan yaduwar annobar a kasarsu ba, duk da cewa za su fuskanci babbar barazanar kamuwa da cutar cikin dogon lokaci mai zuwa.

Ya zuwa yanzu dai kasashen yammacin duniya ba su san dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasarar dakile yaduwar annobar a kasar ba. A cikin bayanin, an rubuta cewa, mutanen Sin da aka yi musu tambaya, wadanda yawansu ya kai kaso 80, sun nuna cewa, idan akwai dama, to suna so a yi musu allura. Sa’an nan mutanen Sin da aka yi musu tambaya, wadanda yawansu ya kai kaso 32, ba su tsai da kudurin a yi musu allura ba tukuna, saboda a ganinsu, ba su fuskantar babbar barazanar kamuwa da cutar. Wasu kaso 79 daga cikin mutanen da suka yi musu tambaya sun bayyana fatansu na a yi musu allura kirar kasar Sin, yayin da wasu kaso 7 ne kadai suka yi fatan a yi musu allura kirar kasashen waje. Ga alama, mutanen Sin ba su tada hankalinsu kan kamuwa da annobar a kasarsu ba. Ban da haka kuma, bayanin ya ambato daukar matakin kulle a wasu biranen da ke lardunan Heilongjiang da Hebei, wanda ya shafi mutane miliyan 6. Amma a ganin marubucin bayanin, irin wannan mataki ya kawo wa kasa da al’umma babban matsin lamba.

Kasashen yammacin duniya ba su ga dalilin da ya sa mutanen Sin ba su kula da harbuwa da annobar ba. Saboda mutanen Sin sun fahimci muhimmancin hadin kai, sun amince da juna, sassa daban daban na kasar sun hada kansu sosai, suna mara wa juna baya a karkashin shugabancin gwamnati. Wasu kasashe suna yin shelar kiyaye hakkin dan Adam. Amma barkewar annobar ta COVID-19 ta tona asirinsu. Al’ummomin Sin ba su kiyaye hakkin dan Adam a baka ba, sun dauki hakikanin matakai wajen kiyaye hakkin al’ummomin kasa duka, alal misali, an dauki tsauraran matakan dakilewa da kandagarkin annobar a kasar Sin. An dauki mabambantan matakai domin fitar da dukkan al’umomi daga kangin talauci a kasar ta Sin. Sabili da haka ne yanzu mutanen Sin ba su nuna damuwa kan yaduwar annobar a kasarsu ba, sun nuna karfin gwiwa kan allura kirar kasar sosai. Sun kuma nuna kyakkyawan fata kan makomar kasarsu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan