logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Cika Alkawarinta Kan Rigakafin COVID-19

2021-02-05 21:12:36 CRI

Ranar 3 ga wata, kasar Sin ta sanar da bai wa shirin COVAX alluran rigakafin COVID-19 miliyan 10, domin biyan bukatun kasashe masu tasowa, lamarin da ya samu babban yabo daga kasashe da dama. Kasar Sin ta cika alkawarinta na mayar da alluran rigakafin a matsayin kayan al’ummar duniya.

Alluran rigakafin da kasar Sin take kai wa kasashen ketare, sun nuna sahihancin kasar Sin a matsayin abokiya ta kasa da kasa. Karin kasashen duniya sun kara fahimtar lamarin. Amma a sa’i daya kuma, wasu kasashe masu kudi sun riga sun saye fiye da rabin alluran rigakafin a duniya, har ma a wasu kasashe, za a yi wa ko wane mutum alluran har sau 5. Abubuwan da kasashe masu sukuni suka yi sun sanya WHO sukar su saboda rashin da’a da suka nuna.

Kananan alluran rigakafin sun nuna babban nauyin da kasar Sin ta sauke. Bisa yaduwar annobar a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da matakanta, tare da fatan karin kasashe za su aiwatar da nasu mataki, domin mara wa WHO baya, a kokarin ganin kasashe masu tasowa sun samu alluran cikin adalci. Fatan dai shi ne, kada son kai ya hana mutane samun nasarar yaki da wannan annoba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan