logo

HAUSA

WHO: Afirka za ta karbi alluran riga kafin COVID-19 miliyan 90 a watan Fabrairu

2021-02-05 09:45:39 CRI

Darekta a hukumar lafiya ta duniya mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti, ta bayyana cewa, kasashen Afirka za su fara karbar kimanin alluran riga kafin COVID-19 miliyan 90, a watan Fabrairun da muke ciki, ta hannun shirin COVAX. Matakin dake zama zakaran gwajin dafi a kokarin nahiyar na yaki da wannan annoba.

A cewar WHO, a ranar 30 ga watan Janairun wannan shekara ce, shirin COVAX ya sanar da kasashen Afirka game da shirin aika musu kashin farko na alluran riga kafin annobar, domin taimakawa shirin yiwa jama’a masu tarin yawa riga kafin annobar a nahiyar.

Jami’ar ta bayyana cewa, kashin farko na allurai miliyan 90, zai baiwa kasashen nahiyar damar yiwa kaso 3 cikin 100 na al’ummominsu dake da hadarin kamuwa da cutar riga kafi a watanni shida na farkon shekara, ciki har da ma’aikatan lafiya, da tsofaffi da wadanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani.

A cewar Moeti, an tsara shirin yiwa a kalla kaso 20 cikin 100 na al’ummun Afirka riga kafi, ta hanyar tabbatar da samar da alluran riga kafin miliyan 600 nan da karshen shekarar 2021.(Ibrahim)