logo

HAUSA

Sin za ta samar da alluran rigakafi miliyan 10 ga shirin COVAX

2021-02-03 19:14:54 CRI

Sin za ta samar da alluran rigakafi miliyan 10 ga shirin COVAX_fororder_20210203-Saminu1-hoto

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta amince ta bayar da gudummawar alluran rigakafin cutar COVID-19 har miliyan 10, ga shirin nan na gaggauta samar da rigakafi mai sauki ga kasashe masu tasowa ko COVAX a takaice, bisa bukatar hakan daga hukumar lafiya ta duniya WHO.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a yau, yayin taron manema labarai da aka gudanar, ya ce hukumar WHO ta fara gudanar da nazari game da tasirin gaggauta amfani da rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ke samarwa, kuma kamfanin samar da rigakafin na Sin, za su ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran abokan hulda, yayin da ake fatan WHOn za ta kammala aikin nazarin rigakafin na Sin ba tare da wani jinkiri ba.  (Saminu)