logo

HAUSA

Shan shayi kullum yana rage barazanar kamuwa da cututtukan magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa

2021-02-07 08:07:46 CRI

Shan shayi kullum yana rage barazanar kamuwa da cututtukan magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa_fororder_src=http___www.ishuocha.com_uploadfile_2018_0319_20180319035707993&refer=http___www.ishuocha

Kwananan baya, wata tawagar masu nazari ta kasar Sin, ta wallafa rahoton nazarinta a mujallar ilmin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya ta Turai, inda suka nuna cewa, shan shayi kullum yana amfanawa lafiyar magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa, tare da rage yawan mace-macen mutane sakamakon cututtuka masu nasaba da magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa, musamman ma ga mutanen da suka dade suna shan shayi, maza masu sha’awar shan shayi, mutanen da suke shan koren shayi

Masu nazarin na kasar Sin sun tantance bayanan da suka shafi mutane fiye da dubu 100, inda suka gano cewa, in an kwatanta da mutanen da ba safai su kan sha shayi kullum ba, mutanen da suke shan shayi kullum sun fi cin gajiyar al’adar ta shan shayi, wato barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cututtuka masu nasaba da magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa ya ragu da kaso 20, kana kuma barazanar mutuwa sakamakon wadannan cututtuka ta ragu da kaso 15.

Masu nazarin sun ci gaba da tantance bayanan da suka samu har sau biyu bayan shekaru 8.2, dangane da al’adar shan shayi da mutane dubu 14 da 81 suke da ita. Sun kuma gano cewa, in an kwatanta mutanen da ba su taba shan shayi ba, mutanen da suka dade suna shan shayi sun fi cin gajiyar al’adar kwarai da gaske. Barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cututtukan magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa, da rasa rayuka sakamakon wadannan cututtuka sun ragu sosai.

Har ila yau, an gano cewa, koren shayi ya fi jan shayi amfani wajen kare mutane daga rasa rayukansu sakamakon cututtukan magudanar jinni a zuciya da kwakwalwa, musamman ma maza.

Shin mene ne dalili? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, watakila dalilin da ya sa shan shayi yake amfana wa lafiyar mutane shi ne domin, akwai sinadarin Tea polyphenols masu yawa a cikin ganyayen shayi. A cikin dukkan nau’o’in ganyayen shayi kuma, koren ganyen shayi ya fi yawan sinadaran. Haka zalika kuma, jikin bil-Adam yana sarrafasinadarin na Tea polyphenols cikin gajeren lokaci, kuma ba ya dadewa a sosai a jikin dan Adam, a don haka, ana bukatar shan shayi cikin dogon lokaci domin amfanawa lafiyar jiki. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan