Sin ta samar da ganyen shayi ton miliyan 2.4 a bara
2017-05-19 16:43:35 CRI
Ministan aikin gona na kasar Sin Han Changfu, ya ce kasar, wadda ta fi ko ina samar da ganyen shayi a duniya, ta samar da sama da ton miliyan 2.4 na ganyen shayi a shekarar 2016, wanda shi ne kashi 40 na adadin ganyen shayi da aka noma a fadin duniya.
Da yake jawabi yayin wani taron kasa da kasa karon farko kan baje kolin ganyen shayi a kasar Sin, Han Changfu ya ce, a bara, kadada miliyan 2.87 na kasar Sin ne aka yi amfani da shi wajen noma ganyen shayi.
Kasar Sin ita ce ta fi ko ina a duniya samun cinikin ganyen shayi, inda a bara aka yi amfani da ton miliyan 2 na shayi, wanda ya yi daidai da kowanne mutum guda na adadin al'ummar kasar na shan kilogram 1.5.
Ma'aikatar harkokin gona da gwamnatin lardin Zhejiang ne suka shirya taron da zai gudana tsakanin ranakun 18 da 21 na wannan watan.
Shugaba Xi Jinping ya tura da jawabin taya murna da aka karanta yayin bude taron, yana mai bayyana fatan taron zai wayar da kai game da ganyen shayin gargajiya na kasar Sin, sannan ya habaka, zuwa wani muhimmin dandalin musaya da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)