Ganyen shayi ya bada taimako wajen kawar da talauci
2020-09-06 19:56:15 cri
A watan Afrilu na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci kauyen Jiangjiaping na gundumar Pingli na birnin Ankang na lardin Shaanxi, inda ya nuna cewa, idan an kiyaye muhalli, sai za a iya cin gajiyar albarkatu min indallahi. Ba ma kawai muhalli ya kasance albarkatu min indallahi ba ne, har ma tattalin arziki ne. Garin Jiangjiaping ya samu sauyawa matuka sakamakon dogaro da ganyen shafi, yawan matalauta ya ragu zuwa kashi 0.74% daga kashi 47% na shekarar 2016. A shekaru 70 na karnin da ya gabata, garin ya kafa gonakin shuka ganyen shayi mai fadin muraba'in mita dubu 933, kudin da manoma suka samu ba zai iya biyan kudin sufuri ba.
A shekarar 2014, reshen jami'iyyar JKS a kauyen ya shigo da kamfanin shayi na birnin Xi'an, don ya zuba jarin kudin Sin RMB miliyan 10 da yiwa gonaki gyaran fuska, tare kuma da kafa tsarin sarrafa ganyen shayi 2 mai fadin muraba'in mita dubu 1.
Saboda jagorancin da kamfanin ke bayarwa a kauyen, fannin ganyen shayin ya samu bunkasuwa matuka. Kamfanin Fenghuang mai samar da ganyen shayi ya zama jagorar kauyen na samun kudin shiga, yawan ganyen shayin da ya samar a ko wace shekara ya kai fiye da ton 10, wanda ya samar da kudin Sin RMB fiye da miliyan 8. Matakin da ya taimakawa iyalai 106 masu mambobin 348 dake fama da talauci inda suka fito daga kangin talauci, karin kudin shiga da suke da su a ko wace shekara ya kai RMB Yuan 1000.
Darektan reshen jam'iyyar na kauyen Luo Xianping ya ce, mun samu wadata daga indallahi, kauyen yana shirin gina sabbin gonakin ganyen shayi muraba'in mita dubu 333, za a fitar da ganyen shayin zuwa sauran wurare a kasar Sin a nan gaba. (Amina Xu)