logo

HAUSA

Manoman Lardin Guangxi Sun Yi Kokarin Fita Daga Kangin Talauci Bisa Fasahar Gargajiya Ta Sarrafa Shayi

2020-08-21 10:29:27 cri

Manoman Lardin Guangxi Sun Yi Kokarin Fita Daga Kangin Talauci Bisa Fasahar Gargajiya Ta Sarrafa Shayi

Kauyen Dachong na yankin Guiping na birnin Hezhou dake lardin Guangxi, wani kauye ne na gargajiya na kabilar Yao. Saboda rashin kyan muhalli da yake da shi, fitar da kauyawa daga kangin talauci a wannan wuri abu ne mai wuya. A shekarun baya-baya nan, kauyawa a wurin sun yi bincike kan fasahar gargajiya ta sarrafa ganyen shayi bisa halin da ake ciki, har ya kai su ga samun wata dabara dangane da hakan, matakin da ya fitar da su daga kangin talauci da samun zaman rayuwa mai wadata.

Mai cinikin shayi Zhou Huafeng na ziyartar dakin Pan Jieyin na kabilar Yao dake kauyen Dachong a kai a kai, don ganin ganyen shayi irin na kabilar Yao guda 520 da ya ajiye a nan. An gina dakin Pan Jieyin ne da tubali da itace dake da tsawo sosai, wanda salo ne irin na gargajiya ta kabilar Yao. A kan zauna a bene na kasa, sannan a ajiye ganyen shayi a bene na sama. Iyalan Pan Jieyin kan hada wutar girki a ko wace rana, inda hayaki kan gasa ginshikan ginin har su canja zuwa launin baki, irin wannan muhalli, ya samar da hali mai kyau na adana ganyen shayi a idanun Zhou Huafeng.

Hayakin abinci ya ba da gudunmawa wajen samar da fasahar tsuma ganyen shayi, matakin da ya sa irin wannan ganyen shayi ke da dandano mai kyau. Saboda haka, masu sayar da ganyen shayi kan je wurin don ajiye ganyen shayi a dakunan kauyawa, matakin da ya kara kudin shiga ga kauyawa kamar Pan Jieyin.

Ya zuwa yanzu, iyalai 12 masu fama da kangin talauci sun shiga wannan sha'ani. Ban da wannan kuma, ganewa ido yadda za a sarrafa da ba da kulawa ga ganyen shayi ya zama abu mai jan hankalin masu bude ido a wannan wuri. (Amina Xu)