logo

HAUSA

An Shigar Da Kayayyakin Tarihi Da Aka Gada Daga Kaka Da Kakanni Cikin Gidajen Al’umma

2021-02-06 19:53:01 CRI

A kwanakin baya, dakunan adana kayayyakin tarihi na sassan kasar Sin sun tsara shirye-shirye masu ban sha’awa da dama domin kara fahimtar da al’umma game da al’adun kasar yayin hutun bikin bazara. Kamar Shirin yawo cikin dakin adana kayayyakin tarihi ta yanar gizo, da samar da kayayyakin al’adu da dai sauransu. Wadannan shirye-shirye da kayayyaki masu ban sha’awa za su kara fahimtar da al’umma game da harkoki da kayayyakin tarihi, ta yadda kowa zai ba da gudummawar yada al’adu da kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, ko wane dakin adana kayayyakin tarihi, babbar makaranta ce. An hada al’adu da tarihin kasar Sin cikin wadannan kayayyaki, don haka, abubuwa ne masu daraja matuka da muka gada daga kaka da kakanni, wadanda suke koyar da mu darussa masu muhimmanci, da kuma kara tabbacin al’umma kan al’adun kasar, yayin da ake ba da gudummawar kyautata zaman rayuwar al’umma. Shi ya sa, ya kamata a karfafa ayyukan gina dakunan adana kayayyakin tarihi, domin su ba da gudummawa kamar yadda ake fata, da kuma shigar da al’adu da kayayyakin tarihi da muka gada daga kaka da kakanni cikin dukkanin gidajen al’ummomi. (Maryam Yang)

Maryam Yang