logo

HAUSA

Babban jami’in diflomasiyya na kasar Sin ya tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka

2021-02-06 16:20:04 CRI

Babban jami’in diflomasiyya na kasar Sin ya tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka_fororder_20210206-Yang and Blinken

Babban jami’in diflomasiyya na kasar Sin, Yang Jiechi, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken.

Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar, ya ce ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Amurka, ya kawo dimbin alfanu ga al’ummun kasashen biyu, tare da inganta zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Ya kara da cewa, dangantakar Sin da Amurka na kan wata muhimmiyar gaba, yana mai cewa, gwamnatin Sin na daukar manufofin da suka dace dangane da Amurka.

Ya ce Sin na bukatar Amurka, ta gyara kurakuran da aka tafka a baya, tare da hada hannu da ita, wajen daukaka ruhin kauracewa rikici da fito-na-fito, da kuma mutunta juna da hadin gwiwar moriyar juna, da mayar da hankali kan hadin gwiwa da hakuri da bambancin dake tsakaninsu, da zummar ingiza kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen.

Har ila yau, Yang Jiechi, ya jaddada bukatar bangarorin biyu, su martaba muradu da tsarin siyasa da hanyar ci gaba da kowannensu ya zaba, da kuma tafiyar da harkokinsu na cikin gida yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha)