logo

HAUSA

WHO: Ana kokarin bin bahasin bayanan da aka samu a kasashe daban daban don gano asalin cutar COVID-19

2021-02-06 16:38:21 CRI

Darekta mai kula da ayyukan gaggawa ta hukumar lafiya ta duniya WHO Maria D. Van Kerkhove, ta bayyanawa wakilin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG a jiya Juma’a cewa, yanzu haka WHO na kokarin bin bahasin bayanan da aka samu a kasashe daban-daban, da nufin gano asalin cutar COVID-19.

A kwanakin baya, wasu nazarin da aka yi, da rahotannin da aka gabatar, sun nuna cewa, an gano alamar kasancewar kwayoyin cutar COVID-19 cikin samfura masu alaka da jikin dan Adam da muhalli, wadanda aka same su a wasu kasashe kafin watan Disamban shekarar 2019. Dangane da batun, Madam Maria ta ce, hukumar WHO tana kokarin bin bahasin dukkan wadannan samfura ta dakunan gwajinta dake kasashe daban-daban.

Ban da wannan kuma, a cewar jami’ar, WHO ta riga ta tuntubi manazarta kimiya da fasaha da suka gano samfuran. Sa’an nan tana neman karin hadin gwiwa da su, da tunanin ayyukan da za a gudanar a nan gaba. (Bello Wang)

Bello