logo

HAUSA

Ya kamata manufofin EU dangane da Sin su kasance masu zaman kansu

2021-02-06 16:47:52 CRI

Ya kamata manufofin EU dangane da Sin su kasance masu zaman kansu_fororder_20210206-France and Germany

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, sun ce ya kamata Tarayyar Turai ta rike matsayinta na mai cin gashin kai tare da samar da manufofinta na kanta dangane da kasar Sin.

Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ke kokarin samar da manufofin bai daya tsakaninta da EU.

Cikin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi, wanda ya biyo bayan taron kwamitin sulhu da tsaron Jamus da Faransa da aka yi ta kafar intanet. Shugaba Merkel ta ce tuni suka fara bin wannan alkibla, bisa yarjejeniyar zuba jari da suka cimma da kasar Sin.

Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a lokacin da aka nemi jin ta bakinsu kan jawabin da shugaban Amurka, Joe Biden ya yi a karon farko kan manufofin kasashen waje, inda ya kira Sin da “babbar abokiyar gasar kasarsa”.

A cewar Angela Merkel, ya kamata manufofin EU kan Sin, su yi la’akari da wasu batutuwa daga Amurka, amma duk da haka, akwai dalilai da dama, kamar na yaki da matsalar sauyin yanayi da sauran wasu batutuwa, da suka ingiza EU yin aiki da kasar Sin, musammam ma saboda batun karfafa huldar kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)