logo

HAUSA

Na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, ta kammala daidaituwa ta 4 bisa falakinta

2021-02-06 17:00:50 CRI

Na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, ta kammala daidaituwa ta 4 bisa falakinta_fororder_20210206-tianwen

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce na’urar binciken duniyar Mars ta Tianwen-1, ta gudanar da daidaituwa karo ta 4 bisa falakinta, a jiya da daddare.

A cewar hukumar, na’urar ta gudanar da daidaituwar ne da misalin karfe 8 na dare agogon Beijing, da zummar tabbatar da cimma tsarin da aka yi na isarta duniyar Mars.

Hukumar ta ce na’urar ta dauki hoton duniyar Mars na farko daga wuri mai nisan kilomita miliyan 2.2

Na’urar wadda aka harba a ranar 23 ga watan Yulin 2020, ta kammala daidaituwa na farko ne a ranar 2 ga watan Augusta, ta biyu kuma a ranar 20 ga watan Satumba, sai ta 3 da ta kammala a ranar 28 ga watan Oktoba.

Na’urar binciken ta yi tafiyar kimanin kwanaki 197, tare da yin nisan kilomita miliyan 465. A yanzu haka, tazarar dake tsakaninta da duniyar bil adama ta kai kilomita miliyan 184, yayin da wadda ke tsakaninta da duniyar Mars ta kai kilomita miliyan 1.1. Dukkan sassan na’urar na cikin yanayi mai kyau. (Fa’iza Mustapha)