logo

HAUSA

Hungary ta amince da amfani da allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar

2021-02-02 15:53:19 CRI

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sanar da cewa, a ran 29 ga watan Jarairu ne, hukumar kula da ingancin magunguna ta kasar Hungary, ta amince da amfani da allurar rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar, wadda ta zama mambar EU ta farko da ta ba da iznin amfani da allurar da Sin ta samar. Firaministan kasar Hungary Orbán Viktor ya bayyana a wannan rana cewa, ya amince da allurar da Sin ta samar. (Amina Xu)