logo

HAUSA

Me Ya Sa Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suke Sauya Ra’ayinsu Kan Rigakafi Kirar Kasar Sin?

2021-02-01 21:46:15 CRI

Kwanan baya, wasu kasashen yammacin duniya, da kafofin yada labarunsu sun sauya ra’ayinsu kan alluran rigakfin cutar COVID-19 da kasar Sin take samarwa.

Ministan lafiya na kasar Jamus Jens Spahn ya ce, muddin EU ta ba da izni, to Jamus za ta yi amfani da alluran rigakafin da kasashen Sin da Rasha suke samarwa ba tare da wata matsala ba. Me ya sa haka? Mako guda ke nan da ya gabata ne wasu kafofin yada labaru suka bayyana cewa, rigakafin da kasashen yammacin duniya suke samarwa ne kawai suke da inganci a duniya. Me ya sa suka canza ra’ayinsu cikin mako guda?

Da ma an shafa wa kasar Sin kashin kaji, wai kasar Sin ta saci bayanan Amurka dangane da rigakafin, sa’an nan an sossoki ingancin rigakafin kasar Sin. Wasu kasashen yammacin duniya suna yunkurin samun riba mafi yawa a kasuwannin duniya ta hanyar sayar da rigakafinsu, sun mayar da rigakafin a matsayin matakin kiyaye danniya. Har ma wasu kasashe masu sukuni sun gaggauta sayen rigakafin fiye da yadda suke bukata. Amma sun yi wa kasar Sin zargi bisa yadda kasar Sin ta bai wa kasashe masu tasowa rigakafin. Sun bata sunan kasar Sin, wai kasar Sin ta yi harkokin jakadanci na rigakafin.

Amma da ganin yaduwar annobar, da kuma matukar bukatar rigakafin, kasashen Turai ba su iya kwantar da hankali ba, suna son sayen rigakafin kasar Sin.

Hakika dai, ba a bambanta rigakafi mai inganci da amfani bisa kasashen da suka kera su ba. Wannan shi ne wani muhimmin dalilin da ya sa karin shugabannin kasashe suka sanya a yi musu alluran rigakafin kasar Sin. Haka kuma, kasashen duniya sun fahimci cewa, kasar Sin tana daukar hakikanin matakai wajen cika alkawarinta, na mayar da rigakafin kamar kayan al’umma na duniya.

Wasu kasashen yammacin duniya ba su bukatar yin kunya, da amince da rigakafin kasar Sin. Ya dace a bar kimiyya ta yi aikinta wajen dakile da kandagarkin yaduwar annobar, lamarin da ya zama wata muhimmiyar fasaha ce da dan Adam zai yi koyi da ita cikin shekara fiye da guda da ta gabata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan