logo

HAUSA

Dubai: Za a samar da allurar rigakafin COVID-19 kirar kasar Sin ga jama’a a kyauta

2021-01-31 16:40:33 CRI

Dubai: Za a samar da allurar rigakafin COVID-19 kirar kasar Sin ga jama’a a kyauta_fororder_dubai

Hukumar lafiya ta Dubai dake cikin hadaddiyar daular Larabawa (UAE), ta sanar a jiya Asabar cewa, daga yau Lahadi, za a fara samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 kirar kasar Sin ga ’yan kasar UAE da mutane mazauna birnin Dubai, ba tare da karbar ko sisin kwabo ba. An ce, za a fara yin allurar ga tsofaffin da shekarunsu suka kai 60 da haihuwa, kafin yiwa sauran mutane riga-kafin.

Kafin haka, asibitocin Dubai suna samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 kirar kasar Amurka da kasar Jamus kawai. Daga bisani, hukumar lafiya ta Dubai ta sanar da cewa, matsalar karancin allurar rigakafin cutar COVID-19 ta sa ta sake tsara ayyukan yiwa jama’a allurar rigakafi. Yanzu an fara yin amfani da allurar kirar kasar Sin ne don samar da karin damammakin yin zabi ga jama’ar kasar UAE, tare da tabbatar da kammala shirin yiwa jama’ar kasar rigakafin cutar COVID-19 cikin wa’adin da aka tsara. (Bello Wang)

Bello