logo

HAUSA

Yadda ake yi wa jama’a alluran riga kafin COVID-19 ya nuna aminci da nagartar alluran kasar Sin

2021-02-01 10:37:31 CRI

Fitaccen masanin cututtukan numfashi na kasar Sin Zhong Nanshan, ya bayyana cewa, yadda ake yi wa jama’a allurar riga kafin da aka samar a kasar, ya nuna cewa riga kafin na da aminci da nagarta.

Zhong Nanshan, ya bayyana yayin kaddamar da wani taro kan inganta amfani da fasaha wajen kandagarki da dakile annobar COVID-19 da aka yi jiya a lardin Guangdong na kudancin kasar Sin cewa, alluran riga kafi 2 da ake amfani da su yanzu haka a kasar Sin, da suka hada da na kamfanin China National Biotec Group da CoronaVac na kamfanin Sinovac Biotech Ltd, dukkansu na da aminci.

A cewar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta kasar Sin, zuwa jiya Lahadi, an yi amfani da alluran riga kafi sama da miliyan 24 a kasar Sin.

Zhong Nanshan ya ce yawan wadanda suke nuna alamomi marasa tsanani bayan karbar riga kafin wadanda suka hada da zazzabi da ciwon damtse da sauran wasu alamomi, ya tsaya ne kan mutum 6 cikin mutane 100,000, yana mai cewa, yawan masu nuna alamomi masu tsanani kuwa, ya tsaya ne kan mutum 1 cikin mutane miliyan 1.

A fannin nagartarsu kuwa, ya ce riga kafin na kasar Sin za su iya kare mutane daga cutar COVID-19 na tsawon akalla watanni 6.

Ya ce yanayin bambancin nagartar riga kafin da gwajin ya nuna a kasashe daban-daban, na da alaka da mabambantan mizani da kasashen suka yi amfani da su.

Ya ce an gudanar da mataki na 1 da na 2 na gwajin alluran riga kafin 2 na kasar Sin ne a cikin gida, yayin da aka yi mataki na 3 a kasashe daban-daban, saboda a lokacin babu masu cutar da yawa a kasar Sin. Yana mai cewa, kasashen sun yi amfani da mizani daban daban, inda a wasu wuraren, galibin wadanda aka yi wa riga kafin, ma’aikatan lafiya ne da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar. (Fa’iza Mustapha)