logo

HAUSA

Kamfanonin samar da riga-kafin COVID-19 guda 7 na kasar Sin sun shiga zagaye na uku na gwajin alluran

2021-01-31 15:42:52 CRI

Jimillar kamfanonin kasar Sin bakwai dake samar da riga-kafin annobar COVID-19 sun shiga zagaye na uku na gwajin alluran riga-kafin, kamar yadda jami’in ma’aikatar kimiyya da fasaha na kasar MOST ya bayyana.

Kawo yanzu, kasar Sin tana da kamfanoni 16 dake aikin samar da riga-kafin annobar COVID-19 inda suke ci gaba da gudanar da gwajin alluran, Wu Yuanbin, darakta janar na ma’aikatar bunkasa kimiyya da fasaha na kasar ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a kwanan nan game da bincike dake shafar gwaje-gwajen jini.

Riga-kafin wanda ba a kai ga kammala shi ba, wanda cibiyar nazarin tsirrai ta Beijing ke shirin samarwa, yana karkashin babban kamfanin kimiyya na kasar Sin CNBG, dake hadin gwiwa da kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar, wanda shi ne na farko da ya samu izinin shiga kasuwanni daga hukumar kula da magunguna ta kasar Sin a watan da ya gabata.

Sakamakon gwajin a zagaye na uku ya nuna cewa ingancin riga-kafin na COVID-19 ya kai kashi 79.34 bisa 100. (Ahmad)