logo

HAUSA

Rukunin farko na rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta bai wa Pakistan kyauta sun isa kasar

2021-02-01 20:29:40 CRI

Da sanyin safiyar yau Litinin 1 ga wata ne, rukunin farko na alluran rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta bai wa kasar Pakistan kyauta suka isa birnin Islambad, babban birnin kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sanar da hakan a yau, yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing. Ya kara da cewa, alluran rigakafin cutar, shi ne rukuni na farko da kasar Sin ta bai wa wata kasar waje kyauta.

Baya ga Pakistan, kasar Sin tana kokarin bai wa wasu kasashe 13 masu tasowa alluran rigakafin kyauta. Kaza lika nan gaba, za ta kara bai wa wasu kasashe 38 masu tasowa, wadanda suke bukatar rigakafin, wadannan alluran rigakafin kyauta. (Tasallah Yuan)