logo

HAUSA

Aikebaier Abulaiti: ba a tilasta wa ’yan kananan kabilu su yi aiki a Xinjiang

2021-02-01 20:27:43 CRI

A yayin taron manema labaru da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya dangane da batun Xinjiang a ranar 1 ga wata, wani saurayi mai suna Aikebaier Abulaiti, wanda ke aiki a wata masana’antar sarrafa harawa a yankin Aksu na jihar Xinjiang ya bayyana cewa, kwanan baya, abokansa da shi kan sa sun san cewa, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, ana tilasta wa ’yan kananan kabilu su yi aiki a Xinjiang. Matashin ya ce wannan maganar banza ce kawai.

Aikebaier Abulaiti ya kara da cewa, shi da abokansa, suna aiki ne domin neman kudi, a kokarin kara kyautata rayuwarsu. Ba wanda ke tilastawa wani yin aiki, kuma babu bukatar a tilasta musu. Don haka ya dace Mike Pompeo ya daina yin irin wadancan maganganu na karya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan