logo

HAUSA

Jami’in yankin Xinjiang ya karyata zargin da Pompoe ke yi na aikata kisan kare dangi da keta hakkin bil-Adama a yankin

2021-02-01 15:09:20 CRI

Mataimakin shugaban sashen fadakar da jama’a na kwamitin JKS na yankin Xinjiang Xu Guixiang, ya karyata zargin da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kitsa cewa, wai ana aikata kisan kare dangi da ayyukan cin zarafin bil-Adama a yankin.

Xu wanda ya karyata wannan zargi yayin taron manema labarai da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya ce, saboda girman wannan zargi da Pompoe ya kitsa a tarihi bil-Adama, yankin yana gayyatar jama’a daga kasashen waje da su ziyarci yankin, don ganema idonsu zahirin abubuwan dake faruwa.

Ya ce, kalaman na Pompeo sun saba dokoki da ka’idar alakar kasa da kasa, kuma tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ya bata ran dukkan kabilun dake Xinjiang. A don haka, matakin nasa shirme ne kawai.(Ibrahim)