logo

HAUSA

Karyar tilasta yin aikin dole a Xinjiang da kasashen yamma suka yi abun dariya ne kawai

2021-01-29 20:24:55 CRI

Karyar tilasta yin aikin dole a Xinjiang da kasashen yamma suka yi abun dariya ne kawai_fororder_2

A yankin Xinjiang na kasar Sin, akwai wata karin magana wai burodin Nang da aka saya da kudin shigar da aka samu ya fi kamshi, ma’anar ita ce, dole ne sai an yi aiki kafin a samu wadata, amma wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma, sun musunta kokarin da al’ummun yankin suke domin kyautata rayuwarsu, har sun mayar da aikin da al’ummun yankin Xinjiang ‘yan kabilar Uygur ke yi a matsayin aikin dole da aka tilasta musu, kuma suna haka ne domin lalata huldar dake tsakanin kabilun kasar Sin, tare kuma da shafawa yankin Xinjiang bakin fenti, da ma nemam hana ci gaban yankin.

A kwanan baya masanin harkokin kasa da kasa na kasar Amurka Einar Hans Tangen ya kalli bidiyon da ‘yan jaridar New Yirk Times suka dauka a birnin Kuitun na yankin Xinjiang, daga baya ya bayyana cewa, “An yi sharhi na nuna son rai, kuma murya ba ta fito ba, kamar wasan kwaikwayon da aka shirya domin nuna muggun nufi.”

Shin wane yanayi al’ummun yankin Xinjiang suke ciki yayin da suke samun aikin yi? Bari mu duba alkalaman da aka yi amfani da su.

Takardun da aka gabatar a fili sun nuna cewa, a baya yankin Xinjiang ya taba fama da kangin talauci mai tsanani, a shekarar 2014, yawan mutanen dake fama da talauci da aka yi musu rajista a yankin ya kai miliyan 3 da dubu 131 da dari 8, domin kyautata rayuwarsu, gwamnatin yankin ta yi kokarin kara samar musu da aikin yi, al’ummun yankin ‘yan kabilu daban daban suna iya zabar aiki da wurin aiki kamar yadda suke so, suna kuma iya samun albashi bayan kulla kwangilar aiki da kamfanin da abin ya shafa bisa doka.

Karyar tilasta yin aikin dole a Xinjiang da kasashen yamma suka yi abun dariya ne kawai_fororder_3

Wasu al’ummun yankin sun fi son fita waje domin yin aiki a sauran lardunan kasar ta Sin, saboda yin aiki a yankuna masu ci gaba, zai ba su damar samun karin albashi, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, matsakacin kudin shigar wadannan ma’aikatan a ko wace shekara, ya kai kudin Sin yuan kusan dubu 40, wadanda suke aiki a cikin yankin Xinjiang su ma suna samun yuan wajen dubu 30 a ko wace shekara, ya zuwa tsakiyar watan Nuwamban shekarar 2020, an cimma burin fitar da daukacin al’ummun yankin daga kangin talauci daga dukkan fannoni.

Sabbin alkaluman da aka fitar ba da dadewa ba sun nuna cewa, matsakacin kudin shigar ko wanne mutumin yankin Xinjiang, ya karu da yuan 6986 idan aka kwatanta da shekarar 2015, wato ya karu da kaso 7.2 cikin dari a ko wace shekara, lamarin da ya nuna cewa, al’ummun yankin Xinjiang suna cin gajiyar ci gaban yankin, hakan ya sake shaida cewa, karyar masu nuna adawa da kasar Sin na kasashen yamma game da yankin abin dariya ne maras tushe kawai.(Jamila)