logo

HAUSA

Sin na fatan wasu jami’an gwamnatin Biden za su martaba ci gaban Xinjiang

2021-01-28 20:08:01 CRI

Yau Alhamis yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya sake karyata kalaman wasu jami’an kasar Amurka kan yankin Xinjiang na kasar Sin, inda ya jaddada cewa, babu manufar kisan kare dangi a kasar Sin, kasar Sin tana fatan wasu jami’an gwamnatin Biden za su martaba shaidu wato yankin Xinjiang yana samun ci gaba yadda ya kamata.

Jami’in ya yi nuni da cewa, a halin yanzu yankin Xinjiang yana cikin yanayi mafi kyau a tarihi na samun wadata, ganin yadda ya samu babban sakamako da ba a taba ganin irinsa a baya a fannin ci gaban zamantakewar al’umma da kyautata rayuwar jama’a. Kana yanayin da suke ciki, shaida ce mai karfi da ke karyata kalaman wasu ‘yan siyasa masu nuna adawa da kasar Sin. A don haka, duk wani yunkuri da suke yi na bata sunan kasar Sin, ba zai kawo illa ga ci gaban yankin Xinjiang ba.(Jamila)