logo

HAUSA

Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta fitar da rahoton kare hakkokin jama’a a bangaren masakun jihar

2021-02-01 14:28:50 CRI

Jihar Xinjiang ta Uygur, mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta wallafa wani rahoton kare hakkokin jama’a a bangaren masakun jihar, wanda ya gabatar da tarihi da ci gaban bangaren da kuma muhimmancinsa ga rayuwar jama’a.

Kungiyar masu masaku ta Xinjiang ce ta fitar da rahoton, da zummar fayyace gaskiya da gina kafofin tuntuba tsakanin Sinawa da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, bisa manufofin bai daya da moriyar juna.

Bayan shekaru 70 da kafuwarsa, bangaren masakun Xinjiang, ya zama mai muhimmanci ga al’ummun dukkan kabilu a yankin, da ma masaku da masana’antun samar da tufafi na kasar Sin da duniya baki daya.

Bangaren ya samu gagarumin ci gaba wajen samar da ayyukan yi da kara kudin shigar manoma da bada gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin jihar da ma inganta rayuwar jama’arta.

Shekara 33.7 ne matsakaicin shekarar ma’aikaci a bangaren. Dukkan ma’aikatan da aka zanta da su cikin rahoton, sun ce sai da sassan kula da ma’aikata suka duba katunansu na shaidar dan kansa, domin tabbatar da shekarunsu ba su gaza 16 ba, wadda ita ce shekara mafi karanci ta aiki da dokar kwadago ta kasar ta tanada.  

Dukkan kamfanoni 26 da aka nazarta cikin rahoton, na da wurin cin abinci na halal, kuma suna bayar da nau’ikan abincin kananan kabilu domin cimma bukatun ma’aikata daga dukkan kabilu. 

Kamfanonin masaku a Xinjiang, na aiwatar da tsarin biyan albashi daidai da aikin da ma’aikaci ya yi, kana sun haramta wariyar jinsi. (Fa’iza Mustapha)