logo

HAUSA

Yawancin allurar rigakafin cutar COVID-19 suna da inganci da tsaro

2021-01-30 21:10:30 CRI

Yanzu, wasu mutanen Najeriya suna damuwa kan ingancin allurar rigakafin cutar COVID-19 da ake amfani da su a wasu kasashen duniya. Sabo da haka, kwanakin baya, a yayin taron dandalin tattaunawa na gwamnonin jihohin arewacin Najeriya, gwamnonin sun tsai da kudurin cewa, idan jihohinsu sun samu allurar rigakafin COVID-19, wato Korona, za su nemi a yi musu allurar domin kokarin kwantar da hankalin jama’arsu.

Yawancin allurar rigakafin cutar COVID-19 suna da inganci da tsaro_fororder_210130-sharhi-hoto3

A hakika dai, fara amfani da allurar rigakafin cutar COVID-19 a duk fadin duniya, wani albishir ne ga daukacin bil Adam, ciki har da jama’ar Najeriya. Amma kamar yadda aka saba, a lokacin da wani sabon abu ya fito a duniya, tabbas a kan samu jita-jita iri daban daban. Bayan da aka fara nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, jita-jita game da ita sun yadu a duk fadin duniya. Alal misali, an ce, “Ashe, an shafe shekaru masu dimbin yawa ana fama da cututukan Aids da Malariya da Kansa da zazzabi iri iri, amma har yanzu ba a samu allurar rigakafi da kuma shawo kansu ba tukuna. Annobar cutar COVID-19 ta bullo shekara daya kawai, ba zai yiyu a samu allurar rigakafin cutar ba.” Har ma wasu su kan ce, “wasu kasashe sun yi nazari da kuma samar da allurar rigakafin cutar domin yunkurin hallaka mu kawai.” Wasu mutanen Najeriya suna shakkar dukkan alluran sabo da wasu yaran kasar sun mutu sakamakon shan allurar rigakafin cutar shan inna da kamfanin Pfizer na kasar Amurka ya samar.

A hakika dai, sabo da babu isashen lokacin nazari da kuma gwada allurar, wasu kamfanonin hada-hadar magunguna sun samar da allurar a kasuwar duniya bisa umurnin da wasu gwamnatocin kasashen yammacin duniya suka ba su ko da yake ba su kammala aikin gwajin allurar na matakai uku ba. Sakamakon haka, allurar ba ta yi amfani kamar yadda ake fata ba. Alal misali, mutane dubu 12 na Isra’ila sun samu allurar da kamfanin Pfizer na kasar Amurka ya samar, amma allurar ba ta yi aiki ba, har ma sun sake kamuwa da cutar. Tsoffi 23 na kasar Norway sun mutu sabo da an yi musu allurar ta kamfanin Pfizer. Sakamakon haka, yanzu ana shakkar inganci da tsaron allurar Pfizer. Bugu da kari, an yi wa mutane miliyan 4 na kasar Amurka allurar da kamfanin Moderna ya samar, wasu daga cikinsu sun kamu da borin jini da cutar shanyewar fuska, har ma wasu sun suma. Sakamakon haka, kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta ba da umurnin dakatar da amfani da ita cikin gagawa.

Yawancin allurar rigakafin cutar COVID-19 suna da inganci da tsaro_fororder_210130-sharhi-hoto2

Amma a hakika dai, galibin allurai, ciki har da alluran da kamfanin SinoPharm da na SinoVac suka samar, suna da inganci da tsaro. Ya zuwa ran 26 ga watan, an riga an yi wa Sinawa miliyan 22.767 allura, kuma babu wani da ya kamu da matsala, balle mutuwa. Jiya an yiwa mata ta allurar da kamfanin SinoPharm ya samar, ba ta kamu da kowace irin matsala ba. Yau ita da diyyarmu sun tafi karkarar Beijing sun sha iska sun hau dutse.

Ko shakka babu, dole ne a mai da hankali sosai a lokacin da ake yi wa wani allurar. Alal misali, idan ana da ciwon hawan jini, ko mace mai ciki da wadanda su kan kamu da matsala ga wasu magunguna, da tsofaffin da shekarunsu ya wuce 60, yanzu kada a yi musu allura. Sannan dole ne wadanda aka yi musu allurar su zauna a inda aka yi musu allurar na tsawon rabin awa, ta yadda za a iya sa ido kan lafiyarsu.

Yanzu, alluran rigakafin cutar COVID-19 da kamfanonin kasar Sin suka samar sun samu karbuwa sosai a cikin gida da kuma a ketare. Wasu shugabannin kasashe da dama sun riga sun samu alluran kasar Sin. Kwararru jami’an kiwon lafiya na kasar Japan ma suna fatan gwamnatin kasarsu za ta yi watsi da allurar da kamfanin Pfizer ya samar, ta yi la’akari da sayen alluran kasar Sin.

Yawancin allurar rigakafin cutar COVID-19 suna da inganci da tsaro_fororder_210130-sharhi-hoto1

A watan da muke ciki, an yi wa shugabannin kasashen Seychelles da Indonesiya allurar da kamfanonin kasar Sin suka samar wa kasashensu. Har ma shugaban Indonesiya Joko Widodo ya yada bidiyo game da yadda aka yi masa allurar. Bugu da kari, shugaba da mataimakinsa da ministan harkokin wajen kasar Turkiya da shugabannin kasashen Serbiya da Kambodiya da Aljeriya da Malasiya da Peru da Chile da Philippines da Hungary sun bayyana cewa, kasashensu za su shigar da alluran kasar Sin.A ran 28 ga watan, an isar da allurar da kamfanin SinoVac ya samarwa kasar Chile. Shugaba Sebastián Piñera Echenique na kasar, da kansa ya yi maraba da allurar da hannu bibbiyu a filin jirgin sama, inda ya bayar da jawabin cewa, allurar da kamfanin SinoVac ya samar tana da muhimmanci matuka, ta kasance kamar wani haske dake cikin duhu.

Kawo yau, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 128674, har ma 1577 daga cikinsu sun mutu a kasar Najeriya. Ko da yake, alluran rigakafin cutar COVID-19 ba su iya shawo kan cutar gaba daya a duk fadin duniya cikin gajeren lokaci ba, amma idan an yi amfani da su, tare da ci gaba da daukar matakan sanya takunkumin baki da hanci da wanke hannu a kullum, da kuma sassauta taruwar jama’a, tabbas za a iya rage damamakin kamuwa da cutar. Muna fatan abokanmu na Najeriya za su iya ba da amsa ga kiran gwamnonin jihohin arewacin kasar. Da jihohin sun samu alluran rigakafin cutar, za su iya amincewa da allurai, ta yadda za a iya hanzarta sassauta halin da ake ciki, har ma za a iya shawo kan cutar baki daya a kasar. Hakan zai iya bai wa ma’aikatanmu Hausawa wadanda suke aiki a sashenmu damar komawa gida domin haduwa da iyalansu. Mu ma za mu iya sake komawa Najeriya domin ganawa da abokan masu sauraronmu. (Sanusi Chen)