logo

HAUSA

WHO na fatan za a hanzarta samar da rigakafin COVID-19

2021-01-12 11:39:37 CRI

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sha alwashin aiwatar da wasu matakai, da za su ba da damar hanzarta samar da karin alluran rigakafin cutar COVID-19 masu inganci, tare da tabbatar da rarraba su daidai gwargwago ga dukkanin sassan duniya.

Mr. Tedros ya ce, yana da shirin yin kira ga daukacin sassan kasa da kasa cikin makon dake tafe, da su cika alkawuran da suka dauka karkashin shirin nan na COVAX, wanda a karkashin sa kasashe daban daban, da hadin gwiwar WHO suka amince za su tabbatar da an rarraba rigakafin COVID-19 ga dukkanin sassan duniya ba tare da wata wariya ba.

A daya bangaren kuma, Tedros ya yi kira ga kamfanonin dake sarrafa alluran rigakafin wannan cuta a sassan duniya daban daban, da su kara azamar samar da alkaluma ga WHO, da za su baiwa hukumar damar gane wadanda za su iya samar mata da alluran ga sassan dake da bukatar gaggawa.

Yayin da duniya ke kokawar shawo kan wannan annoba, tuni wasu kasashe suka fara yiwa al’ummun su rigakafin cutar, bayan samun amincewar hukumomin lafiya da ingancin su.   (Saminu)