logo

HAUSA

An yi wa mutane allurar rigakafin cutar COVID-19 fiye da miliyan 9 a kasar Sin

2021-01-10 17:03:42 CRI

An yi wa mutane allurar rigakafin cutar COVID-19 fiye da miliyan 9 a kasar Sin_fororder_A

Mataimakin shugaban kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin, kana jami’i mai kula da aikin samar da allurar rigakafin cututtuka, mista Zeng Yixin, ya bayyana a jiya Asabar cewa, tun daga ranar 15 ga watan Disamban bara, aka fara gudanar da aikin yi wa mutanen da suke fuskantar hadarin kamuwa da cutar COVID-19 allurar rigakafi. Kawo yanzu, an yi allurar rigakafin da yawansu ya kusan kaiwa miliyan 7.5 kan wadanda ke fuskantar hadarin kamuwa da cutar. Ban da wannan kuma, an taba yin allurar rigakafin da suka kai fiye da miliyan 1.6 kafin a kaddamar da aikin a hukumance, don haka zuwa yanzu an riga a yi wa mutane allurar rigakafin cutar COVID-19 da yawansu ya kai fiye da miliyan 9 a kasar Sin.

A cewar jami’in, yayin da ake gudanar da aikin yin allurar rigakafin, an kafa ka’idojin da ake bi wajen tsara wurin da ake gudanar da aikin, da horar da likitoci masu kula da aikin allurar, da tantance mutanen da za a yi musu allurar, da kula da mutanen da ba su jin dadi bayan an yi musu allurar rigakafin, da dai sauransu, don tabbatar da cewa an gudanar da aikin allurar rigakafin cutar COVID-19 yadda ya kamata.

Zeng ya kara da cewa, yadda aka yi allura har fiye da sau miliyan 9 a kasar Sin, ya shaida inganci da tsaro na allurar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar. Sa’an nan tun da yanzu ana iya samar da karin allurar rigakafi a cikin kasar, za a kara samar da allurar rigakafin ga jama’ar kasar, ba tare da karbar kudi ba. Kana za a aiwatar da aikin bisa nagartaccen tsari, don tabbatar da dukkan mutunen da suka dace an yi musu allurar rigakafin. Ta yadda za a hana yaduwar cutar COVID-19 a kasar bisa samar da garkuwa ga jikin dan Adam. (Bello Wang)

Bello