logo

HAUSA

Peru ta sanar da yin odar allurar rigakafin COVID-19 daga kamfanin Sin

2021-01-07 16:27:59 CRI

Shugaban kasar Peru Francisco Sagasti ya gabatar da jawabi ta gidan talabijin din kasar, inda ya sanar da jama’ar kasar a ranar 6 ga wata cewa, kasar Peru ta cimma yarjejeniya da kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinopharm, domin sayen sabon rigakafin da kamfanin ke kokarin samarwa. Kashin farko na alluran miliyan guda ne ake sa ran za su isa Peru cikin wannan wata.

Sagasti ya ce, an kammala gwajin alluran zagaye na 3 na sabon rigakafin wanda kamfanin hada magungunan na kasar Sin ya gudanar a kasar Peru kuma gwajin ya nuna cewa, rigakafin na da inganci.(Ahmad)