logo

HAUSA

Brazil ta yi odar allurar rigakafin COVID-19 miliyan 100 daga kamfanin Sin

2021-01-08 17:03:02 CRI

Kasar Brazil ta sanya hannu kan yarjejeniya da cibiyar nazarin magunguna ta Butantan dake Sao Paulo, domin sayen alluran rigakafin annobar COVID-19 kimanin miliyan 100, na kamfanin Sinovac na kasar Sin, ministan lafiyar kasar Brazil Eduardo Pazuello, ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Cibiyar Butantan za ta samar da kimanin alluran miliyan 46 ne kafin karshen watan Afrilu, kana ragowar miliyan 54 za su kammala ya zuwa karshen shekarar nan, in ji minista Pazuello, wanda ya bayyana a taron manema labarai.(Ahmad)