logo

HAUSA

Wane alheri takardar bayanan Sin ke dauke da shi game da huldarta da kasa da kasa?

2021-01-11 15:45:33 CRI

Wane alheri takardar bayanan Sin ke dauke da shi game da huldarta da kasa da kasa?_fororder_微信图片_20210111150917

Masu hikimar magana na cewa, “zo ka ci abinci ya fi abincin dadi”. A lokuta da dama gwamnnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta sha nanata kudirinta na kyautata cudanya da kasa da kasa, da ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, gami da bayar da babbar gudunmawa ga ci gaban al’ummar duniya. A karshen wannan mako ne gwamnatin Sin ta fidda takardar bayanai game da batun ci gaban huldarta da kasa kasa. Takardar bayanan, mai taken “Ci gaban huldar kasar Sin da kasashen duniya a sabon karni," ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya fidda takardar. Mai kunshe da babi takwas, takardar bayanan ta fayyace ra’ayoyin kasar Sin game da ci gaban hadin gwiwarta da kasa da kasa a sabon zamanin da muke ciki, da matakan da kasar ta riga ta dauka, da kuma shirye-shiryenta dake tafe a nan gaba.

A cewar takardar, kasar Sin tana ci gaba da kara matsayin hadin gwiwarta da kasashen duniya, tana kara bayar da fifiko ga kasashen dake da karancin ci gaba a nahiyoyin Asiya da Afrika, da kuma kasashe masu tasowa dake karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Tun bayan gabatar da shawarar“ziri daya da hanya daya”, kasar Sin take cigaba da bunkasa kulla alakarta da bada gudunmawa ga fannonin tsara manufofin ci gaban bil adama, da samar da kayayyakin more rayuwa, da cinikayya, da hada hadar kudi, da kyautata alaka a tsakanin mutum da mutum bisa ga bukatun dake shafar kowane bangare na kasashen duniya, da samar da yanayi da damammaki don bunkasa ci gaba da samar da makoma mai haske ga dukkan bil adama a karkashin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ko da yake, wannan ba bakon al’amari ba ne domin kuwa, a lokuta da dama shugaba Xi Jinping ya sha nanata yin kira da a hada hannu domin gina duniya mai wadata. Shugaban ya sha bayyana cewa kasar Sin ta shirya yin aiki da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai wadata da cin gajiyar cigaba na bai daya don samar da makoma mai kyau ga dukkan bil adama. (Ahmad Fagam)

Ahmad Fagam