logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a dauki shekarar 2021 a matsayin ta waraka

2020-12-30 11:20:12 CRI

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya yi kira ga al’ummun duniya da su dauki shekarar 2021 a matsayin ta samun waraka.

Cikin wani sakon bidiyo, sakatare Janar din ya ce, ya kamata jama’a su aminta da juna da kuma yanayin da muhalli, da magance matsalar sauyin yanayi da dakile yaduwar COVID-19 tare da mayar da shekarar 2021 a matsayin ta waraka.

Ya ce ya kamata kudurin shekarar 2021 ya kasance waraka daga tasirin COVID-19 da matsalolin tattalin arziki da na al’umma. Kana ya zama waraka daga rarrabuwar kawuna da kuma farfadowar duniya baki daya.

Antonio Guterres ya ce 2020 ta kasance shekarar dake tattare da kalubale da musibu, yana mai cewa COVID-19 ta jirkita rayuwar jama’a, tare da jefa duniya cikin mawuyacin hali.

Ya kara da cewa idan aka hada hannu, tare da goyon bayan juna, wannan kyakkyawan fata za ta isa ko ina a duniya. Yana mai cewa, sauyin yanayi da annobar COVID-19, matsaloli ne dake bukatar gudunmuwar kowa da kowa, a matsayin wata hanya ta samun makoma mai dorewa tare.

Bugu da kari, Sakatare Janar din ya ce babban burin majalisar a 2021 shi ne, gina duniya da babu sinadarin carbon ya zuwa shekarar 2050, inda ya ce kowacce gwamnati da birni da harkar kasuwanci da daidaikun mutane, za su iya taka rawa wajen cimma wannan buri. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza