logo

HAUSA

2020:Namijin Kokarin Kasar Sin A Shekarar 2020 Ya Karfafa Gwiwar Kasashen Duniya

2020-12-30 14:14:26 CRI

Yayin da muke ban kwana da shekarar 2020, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana addabar mutane a wasu sassan duniya. Da sanyin safiyar ranar 26 ga watan Disamban bana, wani jirgin kasa mai dauke da kayayyakin dakilewa da kandagarkin annobar, da sassan mota da kayayyakin lantarki, wadanda masana’antun lardin Hubei suka kera, ya tashi daga birnin Wuhan, babban birnin lardin zuwa birnin Duisburg na kasar Jamus. Wannan shi ne jirgin kasa na 100 da ya tashi daga Wuhan a bana, wanda ke jigilar kaya tsakanin kasashen Sin da Turai.

Hakika Wuhan, wanda aka ayyanawa matakin kulle cikin kwanaki 76 a bana sakamakon annobar, yana samun farfadowa, ya kuma kasance wata alamar farfadowar tattalin arzikin kasar Sin.

A farkon shekarar 2020, lokacin da aka yi fama da annobar COVID-19 mai tsanani a kasar Sin, an dakatar da wasu harkokin tattalin arziki a kasar. Rashin tabbas sakamakon barkewar annobar, da dakatar da mu’amala a tsakanin mutane a duk fadin duniya, da raguwar bukatun cinikayya a duniya, wadanda ba a taba ganin irinsu ba a baya, sun sanya mutane fargabar ko tattalin arzikin kasar Sin zai farfado ko kuma a’a.

Duk da shakkun da aka yi mata, kasar Sin ta tsaya kan aiwatar da manyan tsare-tsarenta, ta dauki matakai ba tare da bata lokaci ba. Tare da goyon bayan al’ummar kasar, gwamnatin kasar Sin ta dauki wasu matakan dakilewa da kandagarkin annobar yadda ya kamata, ta kuma samu nasarar hana yaduwar annobar. Tun daga watan Maris, al’ummomin kasar Sin suka fara komawa bakin aiki da dawo da harkokin kasuwanci da na samar da kayayyaki.

Alal misali, baya ga biyan bukatunta, ya zuwa farkon watan Disamban bana, kasar Sin ta samar wa kasashen duniya abubuwan rufa baki da hanci fiye da biliyan dari 2, da rigunan kariya biliyan 2 da akwatunan gwajin kwayoyin cuta miliyan 800.

Yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin mawuyacin hali, kasar Sin ta zama kasa daya tilo da ta samu ci gaban tattalin arziki a duniya. Jimilar kudaden da aka samu daga wajen sarrafa dukiyoyin kasar Sin wato GDP ta ragu da kaso 6.8 cikin 100 a rubu’in farko na bana, adadin ya karu da kaso 3.2 cikin 100 a rubu’i na biyu a bana, sa’an nan ya karu da kaso 4.9 cikin 100 daga watan Yuli zuwa Satumban bana. Daga watan Janairu zuwa Nuwamban bana, jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri ya wuce kudin Sin RMB yuan biliyan 899.3, wanda ya karu da kaso 6.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara, adadin da ya nuna cewa, kasashen waje suna son zuba jari a kasar Sin. Kana kuma, darajar kayayyakin da kasar Sin ta sayar zuwa ketare ta wuce dalar Amurka biliyan 268 a watan Nuwamba, wanda ya karu da kaso 21.1 cikin 100. Saurin karuwar kayayyakin da kasar Sin take sayarwa zuwa ketare ta karya matsayin bajimta tun bayan watan Maris na shekarar 2018. Kasar Sin ta ba da nata gudummowa wajen samar da isassun kayayyakin masarufi a duniya. Har ila yau, a ranar 21 ga watan Disamban bana, a karon farko, yawan kayayyakin da aka aika a cikin kasar Sin cikin shekara guda ya zarce biliyan 80, wato a ko wace rana ana aika kayayyaki miliyan 200. Wadannan alkaluma sun nuna cewa, kasar Sin ta samu saurin farfadowar harkokin sayayya, kana ta fitar da manoma daga talauci, kuma karuwar kudin shigarsu sun karfafa bukatunsu na yin sayayya, kana kananan birane da yankunan karkara sun kara azama kan yin sayayya ta Intanet.

A ranar 23 ga watan Disamba, Bankin Duniya ya gabatar da rahotonsa, inda ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kaso 2 cikin 100 a shekarar 2020, kuma adadin zai karu da kaso 7.9 cikin 100 a shekarar 2021.

Me ya sa ake da kyakkyawan fata kan ci gaban kasar Sin? Dalilai su ne, kasar Sin ta yi ta bude kofarta ga kasashen ketare. Tana kuma himmantuwa wajen kyautata yanayin zuba jari mai kwanciyar hankali ba tare da wata rufa-rufa ba, inda kuma za a samu sakamakon da ake iya yin hasashe. Har ila yau, kasar Sin ta rika kara azama kan hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban domin samun moriyar juna.

Tsohuwar darektar asusun ba da lamuni na duniya wato IMF madam Christine Lagarde ta yaba wa kasar Sin cewa, tana ta samun ci gaba tare da ba da gudummowarta ga duniya. A ganin ta, kasar Sin wata gada ce da ta hada kasa da kasa tare, ta kuma taimaka wa duniya samun wadata da kyakkyawar makoma.

Kasar Sin, wadda ta samu nasara a kan annobar yadda ya kamata, ta dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, ta kuma bude kofarta ga ketare, kuma za ta ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta a nan gaba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan