logo

HAUSA

Sin ta fidda takardar bayanan cigaban huldarta da kasa da kasa

2021-01-10 15:50:27 CRI

A yau Lahadi gwamnatin Sin ta fitar da takardar bayanai game da batun cigaban huldarta da kasa da kasa.

Takardar bayanan, mai taken “Cigaban huldar kasar Sin da kasashen duniya a sabon karni," ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya fidda takardar.

Mai kushe da babi takwas, akwai bayanin gabatarwa da kuma rufewa, takardar bayanan ta fayyace ra’ayoyin kasar Sin game da cigaban hadin gwiwarta da kasa da kasa a sabon zamanin da muke ciki, da matakan da kasar ta riga ta dauka, da kuma shirye-shiryenta na nan gaba.

A cewar takardar, kasar Sin tana cigaba da kara matsayin hadin gwiwarta da kasashen duniya, tana kara bayar da fifiko ga kasashen dake da karancin cigaba a nahiyoyin Asiya da Afrika, da kuma kasashe masu tasowa dake karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Tun bayan gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasar Sin take cigaba da bunkasa kulla alakarta da bada gudunmawa ga fannonin tsara manufofin cigaba, da samar da kayayyakin more rayuwa, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da raya alaka tsakanin mutum da mutum bisa ga bukatun dake shafar kowane bangare na kasashen, da samar da yanayi da damammaki don bunkasa cigaba karkashin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, a cewar takardar bayanan.(Ahmad)