logo

HAUSA

Masani:AfCFTA za ta kara karfin tattalin arzikin Afirka na yaki da COVID-19

2021-01-07 10:19:55 CRI

Jami’in tsara manufofin cinikayyar Afirka a hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA) David Luke, ya bayyana cewa, yarjejeniyar cinikayya maras shige ta Afirka(AfCFTA), za ta iya kara karfin tattalin arzikin Afirka, koda duniya za ta iya fuskantar wata matsala nan gaba, kamar annobar COVID-19 da ake fama da ita yanzu.

Cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, masanin ya bayyana cewa, cinikaya tsakanin kasashen nahiyar, za ta taimaka wajen magance duk wata irin matsala da duniya ka iya tsintar kanta, kamar annobar COVID-19 da ta kara fito da raunin kasashen nahiyar na dogora kan abokan cinikayyarsu a sauran sassan duniya.

Luke ya ce, idan har aka aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, hakan zai taimaka wajen kara yin takara da jure hanyoyin samar da kayayyaki a yankin, da kara zamanantar da masana’antun cikin gida da na shiyya, ciki har da bangaren lafiya.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya