logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga Amurka ta gaggauta komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran

2020-12-22 14:35:19 CRI

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce ya kamata Amurka ta gaggauta komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran ba tare da wani sharadi ba, sannan ta dage takunkuman da ta sanyawa Iran da sauran masu hulda da ita.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin wani taron ministocin harkokin waje da aka yi ta kafar bidiyo dangane da batun nukiliyar ta Iran, yana mai cewa, idan Amurka ta komawa yarjejeniyar, ita ma Iran sai ta cika dukkan alkawurran da ta dauka cikin yarjejeniyar.

Taron ya gudana ne bisa jagorancin Joseph Borrell, wakilin Tarayyar Turai kan batutuwan kasa da kasa da manufofin tsaro. Ya kuma samu halartar ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif da na Rasha, Sergey Lavrov da na Faransa, Jean-Yves Le Drian da na Jamus, Heiko Maas da kuma na Birtaniya Dominic Raab.

Yayin taron, Wang Yi ya kuma gabatar da wasu shawarwari 4 dangane da batun nukiliyar ta Iran, wadanda suka hada da: tabbatar da kiyaye tanadin yarjejeniyar da komawar Amurka cikin yarjejeniyar da warware sabani bisa adalci da gaskiya yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar da kuma daukar matakan da suka dace kan batutuwan tsaron yankuna. (Fa’iza Mustapha)